1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mayakan IS sun fice daga birnin Ramadi na Iraki

Suleiman BabayoDecember 27, 2015

Sojojin gwamnatin Iraki da ke samu tallafin dakarun kawance sun samu nasarar sake kwace garin Ramadi daga hannun 'yan kungiyar IS masu neman kafa daular Islama.

https://p.dw.com/p/1HUK5
Kämpfe in Ramadi
Hoto: Getty Images/AFP/STR

Mayakan kungiyar IS mai neman kafa daular Islama sun janye daga tungarsu ta karshe da ke birnin Ramadi na kasar Iraki, abin da ke zama nasara mafi girma ga sojojin gwamnati. Dakarun da ke yaki da ta'addanci sun shafi kwanakin da suka gabata suna kazamin fafatawa a wani ginin gwamnati.

Majiyoyin asibiti sun ce jami'an tsaro kusan 100 suka samu raunika lokacin wannan fafatawa. Dakarun gwamnatin na Iraki sun samun tallafin mayaka Musulmai mabiya tafarkin Sunni gami da rakiyar jiragen saman yakin kasashen kawancen da Amirka ke jagoranta. Dakarun na kawance sun kuma kai farmaki biranen Mosul da Fallujah wadanda suka rage a hannun mayakan na IS.