IS ta kashe sojojin Mali 35
November 2, 2019Talla
Rahotanni daga Bamako babban birnin kasar Mali na cewa adadin sojojin da suka mutu a harin ta'addancin ya kai 35. Wannan sabon hari na zuwa ne kasa da wata guda bayan wani hari da ya halaka sojojin Malin har 38 a wasu sansanoni biyu, arewaci da tsakiyar Mali na cikin tsaka mai wuya na hare-haren ta'addanci tun bullar 'yan aware a shekarar 2012.
Duk da cewa akwai sojojin hadin gwiwa da ke yakar ayyukan ta'addanci a kasar Mali, amma har yanzu 'yan bindiga na barazana ga rayuwar fararen hula da jami'an tsaro.