Mayaƙan Iraƙi sun kashe wani ɗan jarida na Amirka
August 20, 2014Talla
Mayaƙan a cikin bidiyon sun nuna wasu mutane rufe da Fuskokinsu, lokacin da suka kashe James Foley, wanda ya ɓace a cikin ƙasar Siriya tun shekaru biyu da suka gabata.
Sun kuma nuna wani mutumin da suka sace, wanda suka ce shi ma, ransa ya ta'allaƙa ne kawai idan Amirka ta daina kai musu farmaki. A martanin da ta mayar fadar White House, ta ce jami'an leƙen asiri na binciken bidiyon don tabbatar da sahihancinsa. Amirka dai na kai farmakin soji kan mayaƙan a Iraƙi, musamman a Mosul, wanda tuni sojojin Iraƙi suka sake karɓe iko da yankin a farkon wannan mako.
Mawallafi: Usman Shehu Usman Edita: Abdourahamane Hassane