Hana shigar da kayan agaji a Gaza ka iya zama laifin yaki
March 19, 2024Majalisar Dinkin Duniya ta ce shardunan Isra'ila da ke hadasa tarnaki wajen shigar da kayan agaji a yankin Gaza, ka iya zama guda daga cikin laifukan yaki.
Kakakin hukumar kare hakin dan'Adam ta Majalisar Dinkin Duniya Jeremy Laurence ne ya bayyana haka, inda yake cewa la'akari da barin wutar da bangarorin masu fada da juna ke yi da kuma tsauraran matakan da Isra'ila ke dauka a yankin Falasdinu, na nuni da cewa ana son amfani da yunwa a matsayin makamin yaki.
Fiye daFalasdinawa miliyan guda ne ke cikin wani mawuyacin hali na rashin abinci mai gina jiki da magunguna, tun bayan da dakarun Isra'ila suka kara matsa kaimi a kokarinsu na kakkabe mayakan Hamas.
Wannan lamarin na zuwa a yayin da ake sa ran cimma matsaya, kan tattaunawar tsagaita buta wuta da bangarorin biyu ke halarta a kasar Qatar.