1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Michelle Bachelet ta yi jawabin farko

Binta Aliyu Zurmi AA/SB
September 10, 2018

Sabuwar shugabar kungiyar kare hakkin bil' Adama ta Majalisar Dinkin Duniya Michelle Bachelet da ta yi jawabinta na farko a wannan Litinin din, ta sanar da damuwarta kan cin zarafin al'umma a duniya.

https://p.dw.com/p/34dWg
August 7 2018 Rede von Michelle Bachelet CIUDAD DE MEXICO Universität  UNAM Catedra
Michelle Bachelet Shugabar hukumar kare hakkin bil Adama ta MDDHoto: imago/V. Rosas

A jawabinta na farko tun bayan soma aiki Michelle Bachelet, ta nuna kaduwa kan halin da ake ciki a sassan duniya kama daga batun rikicin Idlib na kasar Siriya, zuwa halin da Musulmi 'yan Rohingya na kasar Myanmar ke ciki tun bayan barinsu kasar sakamakon tashe-tashen hankula da kisan kare dangi da aka zargi sojojin kasar da aikatawa. Sabuwar shugaban hukumar kare hakin bil-Adama ta majalisar Dinkin Duniya wadda kuma tsohuwar shugabar kasar Chili ce Michelle Bachelet wadda ta yi jawabinta na farko a wannan Litinin din a cibiyar hukumar da ke birnin Jiniva, ta amince ta gana da ministan harkokin wajen kasar Venezuela Jorge Arreaza, wanda zai yi wani jawabi a ranar Talata a gaban Majalisar Dinkin Duniya a birnin Jiniva.

Museo de la Memoria y los Derechos Humanos, Museum der Erinnerung und Menschenrechte, Santiago, Chile
Tsohuwar Shugabar Chili Michelle BacheletHoto: Museo de la Memoria

Madame Bachelet ta soki yadda ake gallazawa tsiraru a kasashe irin su Myanmar ko Bama, da kuma China, kafin ta yi kira ga kasashen yamma da su guji saka katanga tsakaninsu da 'yan gudun hijira masu neman mafaka. Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ne dai ya nada ta a wannan mukamin inda ta canji dan kasar Jordan Zeid Ra'ad Al Hussein da wasu ke sarginsa da yin suka sosai ga shugabanni. Sai dai daga nata bangaren tsohuwar shugabar kasar ta Chili da ta kama wannan sabon aiki nata daga watan Satumba, ta yi kalamai masu sassauci ba tare da zargin shugabanni ba, sabanin yadda wanda ya gabaceta ke yi a cikin jawabansa, inda ta ce za ta kasance mai sauraron abubuwan da ke damun gwamnatoci, sannan kuma a cewarta hukumar kula da kare hakin bil Adama ta Majalisar Dinkin Duniya da yanzu take jagoranta, za ta kasance mai yin sulhu a cikin lamura.

Michelle Bachelet
Michelle BacheletHoto: picture-alliance/dpa/S. Wenig

A gaban jami'ai da dama na diflomasiyya, sabuwar shugabar hukumar kare hakkin bil-Adama ta MDD ta bayyana damuwarta kan halin da 'yan gudun hijira 'yan Rohingya ke ciki, inda ta nemi manyan kungiyoyin kasa da kasa da su samar da cikakkun shaidu kan cin zarafin da aka yi wa al'ummar Rohingya a kasar ta Myanmar ko Bama, domin a gaggauta daukar matakai na gurfanar da wadanda suke da hannu a ciki. Madame Bachelet ta kara da cewa, wannan mataki da kungiyoyin kasa da kasa za su dauka, zai taimaka wa kotun da ke hukunta masu manyan laifuka ta kasa da kasa ta ICC wadda ta ce ta na da hurumin gudanar da bincike kan cin zarafin da aka yi wa Musulmi 'yan kabilar Rohingya, zargin da hukumomin kasar ta Myanmar ke ci gaba da karyatawa.