An shirya yi wa matsalar ta'addanci taron dangi
March 22, 2019Talla
Baya ga Mali, an shirya bai wa gwamnatin Burkina Faso cikakken goyon baya a yunkurin da take na yakar ayyukan masu tayar da kayar baya. Jakadan kasar Afirka ta Kudu a Majalisar Dinkin Duniya Jerry Matjila da ke cikin tawagar, ya ce burinsu, shi ne a kawar da barazanar da ayyukan ta'addanci ke yi ga rayuwar al'umma.
Ya baiyana damuwa kan irin tsekon da suke fuskanta, sai dai ya ce ya zama dole a dauki mataki. Tawagar ta fara isa birnin Bamako na kasar Mali inda za ta kwashi kwanaki biyu tana tattaunawa kan batun tsaron kafin ta karkare ziyarar a birnin Ouagadougou na kasar Burkina Faso..