MDD ta kira taron gaggawa kan rikicin Falasdinu
October 16, 2015Kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya na shirya wani taron gaggauwa a wannan Juma'a domin tattauna batun rikicin baya bayan nan da ya barke tsakanin kasar Isra'ila da al'ummar Falasdinawa inda mutane 39 suka mutu a cikin makonni biyu kawai. Wata majiyar diplomasiyya ta ce kasar Jodan ce ta nemi a gudanar da wannan zama.
Da misalin karfe ukku agogon JMT na wannan Juma'a ce komitin sulhun MDD zai soma zaman nasa inda zai tattauna batun .
Sai dai wasu jami'an diplomasiyya da su ka bukaci a sakaya sunayensu sun kwarmata cewa zai wuya taron ya iya daukar wani mataki a wannan karo illa dai kawai zai yiwu ya fitar da sanarwa ta yin kira ga bangarorin biyu na Falasdinawa da Isra'ilar da su dakatar da fadan da suke yi.
A share daya dai illahirin kungiyoyin Falasdinawa ne suka yi kira zuwa ga gudanar da zanga zanga a ko ina a cikin kasar a wannan Juma'a bayan kammala sallar Juma'ar.