MDD ta shirya taro kan rikicin Sudan
June 19, 2023Majalisar Dinkin Duniya ta ce ayyukan jin kai na tabarbarewa bayan watannin biyu da fara yakin. Taron dai na zuwa ne yayin da aka kulla yarjejeniyar tsagaita bude wuta ta kwanaki uku wanda ya yayyafa ruwan sanyi ga rikicin a birnin Khartoum bayan rashin nasarar da aka samu a yarjejeniyoyin da aka kulla a baya domin bude hanyoyin isar da kayayyakin agaji.
A taron da zai samu halarcin kasashen Masar da Saudiyya da Katar da kungiyoyin Tarayyar Turai da kuma Afirka, ana sa rai ya tattauna batun tallafi ga Sudan da ma kasashen da ke makwaftaka da ita. Ana kuma sa ran kasashen da ke bada agaji su bayyana adadin kudaden da za su bada a matsayin tallafi domin gudanar da ayyukan jin kai.
Ko da yake, mazauna Khartoum da dama dai sun bayyana cewa, sun samu sa'idar jin karar kai hare-hare ta sama da harbe-harbe a wannan Litinin din sai dai ana ci gaba da fuskantar matsalar karancin abinci da magunguna da wutar lantarki da ruwan sha a ma wasu ababen more rayuwa. Alkalumma sun nuna cewa, wadanda suka mutu a rikicin sun haura mutane dubu 2.