1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

MDD ta soki lamirin Nigeria a game da tserewar Charles Taylor

March 29, 2006
https://p.dw.com/p/Bv3q

Majalisar dinkin duniya tare da kasar Amurka sun yi kakkausar suka ga gwamnatin Nigeria bayan samun rahotanni a game da bacewar tsohon shugaban kasar Liberia Charles Taylor wanda ke gudun hijira a kasar ta Nigeria. Sakataren majalisar dinkin duniya Kofi Annan ya bukaci kasashen Afrika ta yamma su cafke Chrles Taylor, su kuma hana masa mafakar siyasa. Kotun kasa da kasa ta majalisar dinkin duniya dake Saliyo na tuhumar Cahrles Taylor da laifuka goma sha bakwai na keta haddi da cin zarafin alúma. Kungiyoyin kare hakkin bil Adama da masu binciken laifuka na kasa da kasa sun yi kashedin cewa tserewar Charles Taylor na iya haddasa rudani da rashin kwanciyar hankali a yammacin Afrika. Kakakin rundunar yan sandan Nigeria Haz Iwendi yace an kame jamiai 22 wadanda ya kamata su kasance a bakin aiki a gidan da Charles Taylor, ana tuhumar su da rashin daá da kuma sakaci da aiki. Shugaban Nigeriar Olusegun Obasanjo ya kafa kwamiti domin gano yadda aka yi Charles Taylon ya tsere daga garin Calabar.