1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Fargabar rashin Ilmi mai nagarta ga 'ya'yan Rohingya

August 27, 2018

Shekara guda bayan tashe tashen hankula da suka tilasta wa 'yan Rohingya tserewa zuwa Bangadesh, MDD ta yi gargadi kan rashin samun ilimi mai nagarta ga yaran Rohingya.

https://p.dw.com/p/33rTg
Bangladesch Priyanka Chopra, UNICEF-Botschafterin | Unterstützung für Rohingya-Flüchtlinge
Priyanka Chopra Jakadiyar zaman lafiya ta UNICEFHoto: Imago/Zuma Press

Yaran wadanda suke wasa a sansanin 'yan gudun hijira na Cox's Bazar da ke kasar Bangaladash wanda kuma ke zama sansanin 'yan gudun hijira mafi girma a duniya, sakamakon yadda mutanen Rohingya suka tsere daga gidajensu a kasar Mynmar saboda tashe-tashen hankula. Kusan mutane milyan guda ke rayuwa godiya ga kasashen duniya wadanda suka taimaki gwamnantin Bangaladash domin 'yan gudun hijiran su samu kayayyakin da suke bukata na rayuwar yau da kullum.

Sai dai Asusun kula da yara na Majalisar Dinkin Duniya, UNICEF ya ce akwai karancin kayan samar da ilimi ga yaran 'yan gudun hijira. Simon Ingram ya shafe watanni shida yana bincike kan batun ga asusun na UNICEF ya yi gargadi kan yanayin da yaran suke ciki da kuma makomarsu:

Rohingya-Flüchtlingslager Kutupalong
Wani yaro Jibo Ahmed daya daga cikin yara 'yan RohingyaHoto: Jibon Ahmed

"Akwai kimanin yara rabin miliyan wadanda suke tsallaken iyaka na Bangaladash da wasu kuma da suka rage a bangaren Jihar Rakhine a Myanmar da ba sa samun ilimin da ya dace. Wannan ana maganar daukacin yara na Rohingya wadanda ilimi da makomarsu da samun abubuwan da ake bukata na rayuwa ke cikin garari."

Ana tura yaran zuwa makarantu, misali a watan Yuli kusan yara 140,000 aka tura cibiyoyin samar da ilimi kimanin 1,200.  Azuzuwa sun cika fiye da kima, babu batun samun ilimi mai nagarta, sannan Simon Ingram ya kara da cewa babu wani abin da aka tanada ga yara wadanda suka haura shekara 14 da haihuwa.

Bangladesch Rohingya-Proteste im Kutupalong-Flüchtlingscamp
'yan gudun hijira 'yan kabilar Rohingya a BangaladeshHoto: Reuters/M.P. Hossain

"Idan aka yi magana da yaran za ka san cewa akwai wani abu a cikinsu na takaici kan makomarsu. Kuma wani abu ne mai hadari a gare su kan makomarsu game  da kuma makomar mutanen Rohingya nan gaba."

Su dai al'umar Rohingya galibi Musulmai sun shafe shekaru suna fuskantar tsangwama daga mabiya addinin Buddha wadanda suka fi yawa a kasar ta Myanmar ko Burma. Jami'an Majalisar Dinkin Duniya sun zargi hukumomin tsaron Mynmar da neman kakkabe al'ummar Rohingya, inda 'yan gudun hijira suka ce jami'an tsaro sun saka wuta a kauyukansu tare kashe wadanda suke gudu daga rikicin. Jami'an tsaron sun zargi 'yan tawayen Rohingya da kona wani ofishin 'yan sanda. Dubban mutane suka tsere zuwa Bangaladash sakamakon rikicin.

Yanzu asusun kula da yara na Majalisar Dinkin Duniya, UNICEF, ya bukaci sauran kasashen duniya su taimaka wa yaran Rohingya yadda za su samu ilimin da ya dace.