MDD ta yi tir da gwanjon jama'a a Libya
November 20, 2017Sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres, ya bayyana kaduwa da rahotannin da suka nuno yadda wasu ke gudanar da cinikin bayi a kasar Libiya, yana mai cewa wannan wani abin tashin hankali ne matuka. Antonio Guterres, ya ce ganin wani faifan bidiyon da ya nuno ana gwanjon wasu bakin haure a Libiya kan dala 400, matsala ce babba da ta fito da wani nau'i na take hakkin bil adama.
Mr. Gutteres ya yi kiran mahukuntan kasar Libiya da su gaggauta hukunta dillalan bakin hauren da aka kama, saboda a cewarsa cinkin bayi dai bashi da muhalli a wannan duniya. Haka nan sakataren na MDD, ya umurci bangarorin majalisar da su ma su gudanar da cikakken bincike kan wannan lamari, tare kuma da samar da ahnyoyin maganta matsalar bakin na haure.