MDD: Yara za su mutu a Kwango
March 9, 2018Talla
Majalisar Dinkin Duniya, ta ce kananan yara sama da miliyan biyu na iya mutuwa a Jamhuriyar Demokradiyyar Kwango sakamakon bayyanar alamun cutar tamowa. Shugaban hukumar kula da agaji na Majalisar ta Duniya, Mark Lowcook wanda ya ce ana iya tabka wannan asarar muddin aka kasa agaza wa yaran, ya yi bayanin cewa zai gana da masu bayar da agaji a Kwangon a makon gobe, musamman a wuraren da lamarin ya fi ta'azzara. Daga cikin yaran sama da miliyan biyu da ke fuskantar hadarin shekawa barzahun, akwai yara dubu 300 a yankin Kasai kadai.