Merkel ta danganta corona da masifar wannan karni
January 21, 2021A lokacin da take bayani ga manena labarai a birnin Berlin, shugabar ta ce duk da hadarin da ke tattare da rikidewa da kwayar cutar ke yi, ya kamata a guji rufe kan iyakoki da kasashen Turai da ke makwabtaka da Jamus. Sai dai ta bada shawarar hada gwiwa tsakanin kasashe dabam-dabam don yaki da annobar gadan-gadan.
Sannan kuma ta ce da zaran an cigaba da samu raguwar masu kamuwa da coronavirus a Jamus, za a fara bude wuraren kula da yara da kuma makarantu.
Yanzu haka kasar ta Jamus na samu raguwa masu kamuwa da cutar a cewar cibiyar Robert Koch, cibiyar ta ce a cikin kwanaki bakwai kasar ta yi kasa sosai a yawan adadin da take samu, irinsa na farko tun a watan Nuwamba bara.
Jamus ta sha alwashi cin galabar wannan cutar kafin karshen wannan shekarar.