Merkel ta yi godo da Serbiya da ta tattauna da Kosovo
August 23, 2011Yayin ziyarar wucin gadin da shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ke yi a yankin Balkans, ta tattauna da shugaban Serbiya Boris Tadic inda ta bayyanawa gwamnati a Belgrade kai tsaye cewa, gyara dangantakar ta da Kososvo na ɗaya daga cikin sharuɗɗan da ƙasar zata cika kafin ta shiga ƙungiyar Tarayyar Turai, wanda Serbiyar ta daɗe tana nema yanzu.
Ita dai Merkel ta jaddada cewa Jamus na matuƙar so Serbiya ta shiga ƙungiyar Tarayyar Turai kasancewar ta ƙasa a Nahiyar Turai. To sai dai shugaba Boris Tadic ya bayyana cewa Serbiya ba zata amince da Kosovo a matsayin 'yantacciyar ƙasa ba. Ya kuma ƙara da cewa ƙasarsa ta yi ƙoƙari sosai wajen aiwatar da mafi yawancin sauye-sauyen da ƙungiyar Tarayyar Turan ta buƙace ta da ta aiwatar, kana ya haƙiƙance a kan cewar yanzu ya kamata a sa ranar da Serbiya zata fara rattaba hannu a kan yarjeniyoyin shiga ƙungiyar.
Mawallafiya: Pinaɗo Abdu
Edita: Umaru Aliyu