Mike Pompeo na ziyara a Saudiyya
April 28, 2018Talla
Ziyarar Pompeo a Saudiyya na da daukar hakali ta fannoni masu yawa, kama daga rikicin Siriya da Yeman, sai kuma uwa uba yadda gwamnatin Trump ke ingiza kiyayya kan Iran daga makobtanta. inda Trump ya sanar da ranar 12 ga watan gobe a matsayin ranr da zai bayyana mataki da matsayinsa kan yarjejeniyar nukiliyar Iran. Yarjejeniyar da kasashen duniya suka cimma da Iran, wace kuma Donald Trump ke matukar sukar lamarin. Daga kasar Saudiyya, sabon sakataren harkokin wajen na Amirka zai zarce Isra'ila da Jordan.