Miliyoyin yara na shakar gurbatacciyar iska
October 31, 2016Talla
Binciken rahoton dai ya nuna cewa irin iska maras tsabta da kananan yaran ke rayuwa a ciki na da mummunar illa da ke haifar da babbar matsala ga kwakwalwar wanda ke yin nakasu ga wasu sassa na halittun jikin yara.
A yanzu dai Majalisar Dinkin Duniya ta ce ana samun yaro guda cikin bakwai a fadin duniya da ke shakar gurbatacciyar iska mai dauke da guba sabanin tsarin da ya dace da hukumar kiwon lafiya ta duniya WHO. Wannan ya sa ake ganin gurbatar yanayi a matsayin abin da ke zama barazana ga rayuwar kananan yara a duniya.
Binciken dai ya nuna cewa yara miliyan 520 a kasashen Afirka da ke fuskantar matsalar gurbatar yanayi na hayakin ababen hawa, da na murhun abinci hade da na kura mai datti da ma dumamar juji.