Ministan tsaron Isra'ila ya yi murabus
November 14, 2018Talla
Ministan tsaron Isra'ila Avigdor Lieberman mai tsattsauran ra'ayin kishin kasa ya soki lamirin yarjejeniyar wacce ya bayyana a matsayin yin saranda ga ta'addanci. Tuni ma ya sanar da ficewar jam'iyyarsa ta Isra'ila Beiteinou daga cikin kawancen masu mulkin, kana ya yi kira da a shirya zaben gaba da wa'adi na 'yan majalisar dokoki da ya kamata a shirya a watan Nuwamban 2019.
Wannan murabus na nufin cewa a yanzu firaministan kasar ta Isra'ila na da karamin rinjaye ne na kuri'a dai tilo a majalisar dokokin kasar, lamarin da ya jefa rudani a game da makomar gwamnatinsa wacce aka kafa a shekara ta 2015 da kuma ake yi wa kallon mafi karfi a tarihin kasar ta Isra'ila.