Mnangagwa: Zimbabuwe za ta shirya sahihin zabe
January 19, 2018Talla
Mnangagwa ya yi wannan tsokaci ne a wata hira da aka yi da shi ta jaridar Financial Times, inda ya ce abun da suke bukata shi ne zabe na gaskiya wanda zai yi kima a idanun duniya, don haka yana son Majalisar Dinkin Duniya da Tarayyar Turai su turo da 'yan kallonsu a zabukan kasar masu zuwa.
Yayin wata ziyara ce dai da ya kai a kasar Mozambique a ranar Alhamis a wani rangadi da ya soma a kasashen yankin, Shugaban na Zimbabuwe Emmerson Mnangagwa ya sanar cewa zabukan kasar za su wakana ne cikin watanni hudu zuwa biyar masu zuwa, inda ya ce zai yi duk abun da ya dace na ganin an yi zabe na gaskiya mai kima.