MPLA a Angola ta sami nasara
September 1, 2012Talla
Masu aiko da rahotannin sun ce a cikin sama da kishi 60 cikin ɗari na ƙuri'un da aka ƙiɗaya , jam'iyyar ta shugaba José Eduardo Dos Santos ta sami kusan kishi 74 yayin da abokiyar hamayyar ta ta UNITA ke da kishi 17 da yan ka.
Wata yar jarida daga birnin Luwanda, ta ce amma duk da haka jam'iyyar adawar ta UNITA ta taka muhimmiyar rawar gani a babban birnin ƙasar.ta ce ''Mutun ɗaya cikin ukku a birinin na Luanda ,sun zaɓi jam'iyyar addawa ta UNITA.''Zaɓen wanda a ƙarƙashin sa za a sami wakilai ɗari biyu a majalisar , ya tanadi naɗa shugaban jam'iyyar da ta yi rinjaye a matsayin shugaban ƙasa.
Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Yahouza Sadissou Madobi