Mugabe ba zai zabi Mnangagwa ba
July 29, 2018Talla
Yayin jawabin da ya yi wa manema labaru a gidansa na birnin Harare, Robert Mugabe ya ce ba zai zabi wanda ya azabtar da shi ba.
Ya kuma yi kiran da a kaurace wa zaben gwamnati mai ci ta Shugaba Emmerson Mnangagwa, ko da yake bai bayyana wanda yake goyon bayansa daga cikin wadanda ke takarar ba.
Wannan ne karon farko da aka sami 'yan takara masu yawa a babban zaben kasar ta Zimbabuwe.
Shugaba Emmerson Mnangagwa dai na fuskantar adawa mai zafi daga matashi Nelson Chamisa.
An kuma yi hasashen samun magudi da ma yiwuwar bijire wa sakamakon zaben.