Mugabe na son mutuwa a kan mulki
December 7, 2014Talla
Haka nan ma jam'iyyar ta zabi mai dakinsa Grace Mugabe a matsayin sabuwar shugabar matan jam'iyyar ta ZANU PF. Hakan dai na nuni da cewa matar ta Mugabe ka iya tsayawa takarar shugabancin kasar domin ta gaji mijinta idan ya sauka daga mulki, kamar yadda ta nuna sha'awar hakan. Jam'iyyar ta ZANU PF dai ta amince da Mugabe da ke da kimanin shekaru 90 a duniya, ya sake tsayawa takarar shugabancin kasar inda zai sake jagorantar mulkin Zimbabuwe na tsahon wasu shekaru hudu masu zuwa. A makon da ya gabata dai mataimakiyar Shugaba Mugabe ta rasa mukamintaa jam'iyyar tasu ta ZANU PF.
Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Pinado Abdu Waba