Mugabe ya fita bainar jama'a
November 17, 2017Dama dai a kowace shekara shugaba Mugabe na halartar bikin kamala karatun digiri na daliban jami'ar karatu daga gida, wato Open Univerty da ke kasar, sai dai a wannan karon 'yan kasar Zimbabuwe sun fidda tsammanin halartar shugaban ganin irin halin matsin lamba da ya tsinci kansa a ciki na daurin talala.
Sai dai har yanzu manyan sojojin kasar tare da wasu wakilan kasashe makota na ci gaba da tattauna batun yuwar yin murabus din shugaba Mugabe daga karagar mulki, yunkurin da ake hasashen zai seta al'amuran siyasar kasar da ke cikin rashin tabbas.
A ranar Laraba da ta gabata ne sojoji suka yi wa fadar shugaba Mugabe mai shekaru 93 dirar mikiya, tare da yi masa daurin talala na hanashi fita yayin da sojojin suka karbe ragamar kafar talabijin na kasa tare da mamaye babban birnin kasar Harare. Lamarin da 'yan kasar da sauran kasashen duniya ke wa kallaon tabbatuwar juyin mulki, amma sojojin suka musanta inda suka ce sun yi haka ne da nufin kakkabe 'yan siyasa da ke yi wa tattalin arzikin Zimbabuwe zagon naksa.