1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Muhawara a kan cikakken hankalin Donald Trump

Abdourahamane Hassane
January 6, 2018

Wani dan jarida ya wallafa sabon littafi a kan Donald Trump wanda aka yi wa la'akabi da sunan: wauta da fushi a fadar White House.

https://p.dw.com/p/2qQVF
Mar-a-Lago Donald Trump
Hoto: picture-alliance/AP/A. Brandon

Michael Wolff wanda shi ne ya wallafa sabon littafin a kan Donald Trump ya ce shugaban na iya nanata magana daya sau uku a cikin mintoci goma. Sannan ya ce wasu daga cikin na kusa da shugaban na da shakku a game da cewar ko yana da cikakken hankali ta yadda zai iya yin mulki. Sakataran harkokin wajen  Amirka Rex Tillerson ya kare shugaban na Amirka daga kallon da ake yi masa na mai tabin hankali yana mai cewar kazafi ne kawai.