Muhawara kan sauya fasalin MDD
September 18, 2017Talla
Kasashe 130 daya baya daya za su gabatar da jawabai inda za su bayyana matsayinsu da ma shawarwari a game da wannan bukata ta Shugaba Trump ta sauya fasalin tsarin aikin Majalisar Dinkin Duniya. A watan Agustan da ya gabata kasar Amirka wacce ke a sahun gaba wajen samar da kudaden gudanarwa ga Majalisar Dinkin Duniya ta nemi goyon bayan wasu kasashe 15 da suka hada da Faransa da Ingila da Jamus da Italiya wajen ganin sun ba ta hadin kai ga cimma wannan buri na yi wa Majalisar Dinkin Duniya gyaran fuska. A gobe Talata ne dai za a soma gabatar da manyan jawabai a babban taron koli na Majalisar inda batun rikicin nukiliyar Koriya ta Arewa da kuma batun sauyin yanayi za su kasance a sahun gaban maudu'an da taron zai tattauna.