Muhawarar tsige Trump a majalisar Dattijai
January 26, 2021Talla
Wannan daftarin dai na tuhumar shugaba Donald Trump da ingiza magoya bayansa su afkawa majalisa a farkon watan Janairu.
Sai dai kafin 'yan majalisar Democrat su cimma burin ganin an hukunta Trump, suna bukatar goyon bayan takwarorinsu na jam'iyyar Republican akalla mutum sha bakwai, lamarin da ake ganin da kamar wuya duk da cewa wasu daga cikin 'yan Republican din basa goyon bayan afkawa majalisar da magoya bayan Trump suka yi.