1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Muhawarar tsige tsohon shugaba Trump

February 11, 2021

Muhawara ta kankama a majalisar dattijan Amirka na shari'ar tsige tsohon shugaban kasar Donald Trump.

https://p.dw.com/p/3pCKA
US-Präsident Donald Trump
Hoto: Saul Loeb/AFP/Getty Images

'Yan Jamiyyar Democrats a majalisar dattijan Amirka sun gabatar da tuhumar haddasa tunzuri akan tsohon shugaban kasar inda suka yi da'awar ikrarin Trump cewa magudin zabe shi ne ya haddasa zanga zangar da ta auku a majalisar dokokin a ranar 6 ga watan janairu da cewa ba shi da tushe balle makama. 

A rana ta farko ta shari'ar a ranar Laraba an nuna faya-fayen Bidiyo da masu gabatar da kara suka ce Trump yana tunzura magoya bayansa su afkawa majalisar dokokin a ranar 6 ga watan Janairu.

Masu tuhumar da kuma bangaren lauyoyin Trump na da saoi 16 kowannensu ya gabatar da bayanansa cikin kwanaki biyu.

Jagoran 'yan Democrats a shariar tsigewar Jamie Raskin ya baiyana shariar da cewa lokaci ne na fayyace gaskiya ga Amirkawa ya kuma yi watsi da da'awar lauyan Trump cewa shugaban ba shi da hannu a zanga zangar.