1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Bala'i

Shekaru 20 da hadarin jirgin ruwa a Senegal

Abdourazak Maila Ibrahim RGB
September 27, 2022

An yi taron tuni da dubban mutanen da hadarin jirgin ruwa ya rutsa da su shekaru 20 da suka gabata a kasar Senegal, inda danginsu ke korafin rashin samun taimako.

https://p.dw.com/p/4HQQL
Senegal Fähre Joola Unglück Schiffskatastrophe 2002
Hoto: picture-alliance/dpa

A kwana a tashi an cika shekaru 20 da jirgin ruwa ya nitse da mutanen da ke kan hanyar fitowa daga hutun karshen shekara tsakanin Dakar da Ziguinchor, wannan ibtila'in ya rutsa da mutum kusan dubu biyu ciki har da yara dari biyar. Sai dai har yanzu 'yan uwan wandada ibtila'in ya shafa, sun nuna cewa taimakon da gwamnati ta yi musu bai taka kara ya karya ba. 

Wasu daga cikin dangin wadanda lamarin ya rutsa da 'yan uwansu na jini, na ci gaba da nuna alhini bayan kwashe shekaru ashirin, Boubacar Ba ya rasa 'yan uwansa hudu a cikin wannan nutsewar jirgin ruwan, wanda kuma da su ne iyalin suka dogara domin tallafa musu a rayuwa. 

Ya ce:  "Wannan rashin na da wuyar jurewa domin dan uwana ya bar gurbi a matsayin shi na mai taimaka mana a rayuwar yau da kullum don haka na ke cewa mun yi  babban rashi wanda ba mu kadai ba har da uwarmu da ke cikin kaduwa har yanzu''

Bayan miliyan goma da gwamnatin ta bai wa iyalai tun bayan hadarin, babu wani tallafi da suka kara samu daga gwamnati a cewar Boubakar Ba.

Khadidiatou Diop ta rasa mahaifiyarta a nitsewar jirgin ruwan, da danta guda da kuma wata yar uwarta ta kusa, ta shaida har kwanan gobe lamarin na damunta sosai musanman idan ta tuna mahaifiyarta: Ta ce:"Daga shekara ta 2002 ya zuwa wannan lokacin, ina ci gaba da yin mafarkinta, ba zan taba mantawa da ita ba"

Khadidiatou Diop a cikin wannan halin na damuwa ta ce, ga dukan alamu gwamnati ta manta da su, a cewar ta babu alamun shigar da kara a gaban kotu domin samun gaskiyar dalilin nutsewar jirgin ruwan bayan shekaru ashirin, saboda haka sun bar wa Allah lamarin.

Albarkacin zagayowar  ranar  tuni da wadanda suka rasa rasu a cikin wannan nutsewar jirgi, taken taron na bana shi ne, "Farfadowa da sauran sassan jirgin ruwan Joola" a tsakanin Dakar da Ziguinchor, sai dai sauran iyalan sun bukaci da ayi zaman makoki ga 'yan uwan su da suka rasu 29.09.2002 shekaru ashirin da suka gabata.