Sudan: Murkushe zanga-zanga da sojan haya
January 11, 2019Masu zanga-zangar a ranar ta Juma'a na kiran cewa 'yanci da zaman lafiya da adalci suke nema; 'yan kasa sun yanke shawarar yin juyin juya hali.
To sai dai ba a jima da fara wannan zanga-zangar a birnin Khartoum ba, sai jami'an tsaro suka tarwatsa zanga-zangar ta hanyar amfani da alburusai masu kisa. Wasu 'yan kasar dai sun ce, sun ga wasu 'yan kasar Rashan da kayan jami'an tsaro suna harbi kan mai uwa dawabi cikin dandazon jama'a kamar yadda wani saurayi ke yadawa ta shafin yanar gizo, yana wa masu zanga-zangar gargadin su yi hattara: "Gwamnatin Sudan ta dauko sojojin haya daga ketare, don su murkushe zanga zanga.Ya kamata kowa ya shiga taitayinsa. Wannan sanarwar mun sameta ne daga wani soja na kwarai.”
Ya zuwa yanzu dai mahukunta sun ce, an kashe kimanin mutane 17 sakamakon zanga zangar, cikinsu har da jami'an tsaro uku sai masu sharhi kan zanga-zangar na cewa adadin ya fi haka.
Dama dai shugaban na Sudan al-Bashir, wanda ke zama shugaban Larabawa na farko da ya kai ziyara ga shugaban Siriya Bashar al-Asad, ana nemansu ruwa a jallo gaban kotun duniya, kan kisan kiyashin al'ummomin kasar.
Kuma an jiyo shugaba al-Bashir din, wanda cikin tsukin shekarar da ta gabta ya kai ziyara har sau biyu zuwa Rasha, an jiyoshi yana cewa, bai barin mulkinsa sai ta hanyar zabe, amma ba ta hanyar zanga-zangar wadanda ya kira 'yan barandar kasashe makiya.