1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bukukuwan karamar salla a kasashe da dama

Gazali Abdou Tasawa
June 4, 2019

Al'ummar Musulmi a kasashe duniya dabam-dabam na gudanar a wanann Talata da bukukuwan sallar azumi ko karamar salla wacce suka saba a kowace shekara.

https://p.dw.com/p/3Jmj3
Eid Fest in Nigeria
Hoto: DW/A. A. Abdullahi

Wannan salla da aka fi sani da suna Eid el-fitr na daga cikin jerin bukukuwan sallar da addinin Islama ya wajabta ga musulmi.

 A bana dai a kasashe da dama kamar Saudiyya da Najeriya da Nijar Muslmin na gudanar da bukukuwan na bana a rana daya bayan da suka ga wata a daren jiya, akasin yadda aka saba gani suna yinsu baram-baram a shekaru da dama a baya. 

Bayan tasowa daga sallar idi a kasashen na Musulmi, bayan shan liyafa ta musamman albarkacin sallar, jama'a za su share tsawon suna ziyartar juna da yi wa juna barka da salla da fatan alkhairi. Sai dai tun a jiya Litinin ne wasu kasashe kamar Mali suka gudanar da bukukuwan sallar azuminsu ta bana.