Mutane 14 sun mutu cikin wani hari a Kabul
June 20, 2016Talla
A Afganistan mutane 14 sun halaka wasu takwas sun ji rauni a cikin wani harin ta'addanci da wani dan kunar bakin wake ya kai kan wata karamar mota kirar safa mai dauke da jami'an tsaron kasar Nepal.
Kakakin ministan cikin gidan kasar ta Afganistan Sediq Seddiqi wanda ya tabbatar da labarin kai wannan hari a kan shafinsa na Tweeter ya ce ya zuwa yanzu suna gudanar da bincike domin tantance mutuman da ya kai harin a birnin Kabul.
Sai dai tuni kakakin kungiyar Taliban Zabihullah Mujahid a shafinsa na Tweeter ya ce kungiyarsu ce ke da alhakin kai harin kan abin da ya kira sojojin mamayar kasar Afganistan.