1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Mutane 17 za su gurfana a gaban kotun Kamaru

Binta Aliyu Zurmi
March 2, 2024

Akalla mutane 17 ne za su gurfana a gaban kotu a bisa zargin marar hannu a kisan dan jarida Arsene Salomon Mbani da aka fi sani da suna Martinez Zogo a kasar Kamaru.

https://p.dw.com/p/4d6iZ
Paul Biya
Hoto: Jemal Countess/UPI/newscom/picture alliance

Sanarwa ta kotun soja da ke Yawunde ta ce daga cikin mutanen akwai shahararen da kasuwar nan Jean-Pierre Amougou Belinga da kuma Maxime Leopold Eko tsohon shugaban hukumar leken asiri.

Marigayin dan jaridar da ya yi shuhura wajen caccakar lamirin gwamnatin Shugaba Paul Biya, amma an samu gawarsa ne kwanaki bayan bacewarsa a  watan Janairun shekarar 2023.

Al'umma da dama a kasar na masu shakkun bi wa dan jaridar hakkinsa bisa la'akari da yadda kasar ta yi suna wajen dakile ayyukan 'yan jarida.

A shekarar da ta gabata 'yan jaridu 3 masu zaman kansu ne aka yi musu kisan gilla a kasar ta Kamaru, a cewar kungiyar human Right watch.