SiyasaJamus
Hargitsi ya rauna mutane 42 a Isra'ila
April 29, 2022Talla
Ma'aikatan agaji sun ce akalla mutune 42 ne suka jikkata, biyo bayan barekewar wata hatsaniya tsakanin 'yan sandan Isara'ila da Falasdinawa masu ibada a harabar sallacin Aqsa a sanyin safiyar wannan Jumma'a.
Rahotanni sun ce tuni aka gargaza da wadanda suka jikkatan zuwa asibiti a cewar ma'aikatan agajin. Wurin mai tsalke da ke tsakiyar Jérusalem na ci gaba da zama wata madigar fitina tsakanin Falasdinu da Isra'la a baya bayan nan, musamman a wannan lokacin na ibada, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane baya ga jikkata wasu da dama.