Mutane 7 na hannu 'yan bindiga a Abuja
September 10, 2020Wasu 'yan bindiga dauke da makamai sun afka wa garin Tungar Maje da ke kusa da Abuja babban birnin tarayar Najeriya, inda suka yi artabu tsakaninsu da ‘yan sanda da suka yi kokarin kalubalantar su. Wasu da abin ya faru a kan idanunsu sun tabbatar da cewa an raunata wasu mutane da dama, yayin da ‘yan banga da ‘yan sanda suka samu kwato wasu da aka yi garkuwa da su, amma a karshe maharan sun yi awon gaba da mutane 7.
Kakakin rundunar ‘yan sanda ta Abuja Anjuguri Mamza ya shaida wa wakilinmu Uwais Abubakar Idris da ke Abuja cewa, lallai an samu matsala a Tungar Maje, amma yana kan rubuta sanarwa da zai aikawa manema labaru. Sai dai wanda bai so a ambaci sunansa ya ce sun shiga halin damuwa a Tungar Maje. Wannan hari ya zo kasa da mako guda bayan bayyana bullar sansanoni na ‘yan ta’adda a kusa da Abuja hedikwatar Najeriya.