Mutane 85,000 sun fice daga Falluja
June 24, 2016Talla
Hukumar ba da agajin gaggawa na MDD ta ce sama da mutane dubu tamanin da biyar 85,000 ne suka fice daga birnin Falluja sakamakon yunkurin da dakarun Iraki ke yi na kwato birnin daga hannun mayakan IS. A cikin wannan watan ne dai sojoji kasar suka tsananta kaddamar da sumame a kan mayakan na IS da nufin kwace iko da birnin Fallujan da 'yan IS din suka kafa tunga a ciki.
Hukumar ba da agajin ta ce, ana sa ran wasu kimanin 60,000 za su iso sansanin Khalidya dan samun mafaka. A yanzu dai akalla sama da mutane miliyan uku ne ke gudun hijira a kasar Iraki a tun watan Janairun shekara ta 2014.