1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mutane 860 suka rasu a hare-hare kan mayakan IS

November 12, 2014

Mambobin kungiyar nan ta Nusra ta Siriya da ke da alaka da kungiyar Al-ka’ida da fararen hula ciki kuwa har da mata da kananan yara na cikin wadanda lamarin ya rutsa da su.

https://p.dw.com/p/1Dls8
Symbolbild Islamischer Staat
Hoto: Getty Images/K. Cucel

Masu fafutuka da ke sanya idanu a rikicin kasar Siriya sun bayyana cewa sojojin hadaka karkashin jagorancin Amurka sun hallaka mayakan IS da ma wasu 'yan tawaye da ke mara musu baya 860 ciki kuwa har da fararen hula tun bayan lugudan wutar da aka fara kan mayakan a tsakiyar watan Satimba.

Wannan kungiya da ke da sansani a Birtaniya ta bayyana cewa cikin adadadin, mafi rinjaye wato wadanda aka kashe 746 mambobi ne na mayakan na IS inda 60 kuma suka kasance mambobin kungiyar nan ta Nusra ta Siriya da ke da alaka da kungiyar Al-ka'ida inda ragowar 50 suka kasance fararen hula da suka hada da mata biyar da kananan yara takwas.

Tun dai daga ranar 23 ga watan Satimba aka kaddamar da hare-haren kan mayakan na IS a kokarin dakile ayyukan su bisa ayyukan sojojin kawance na kasashen duniya bisa jagorancin Amirka.

Mawallafi: Yusuf Bala
Edita: Suleiman Babayo