Mutane aƙalla 26 ne suka rasu a hare-hare a Iraƙi
October 16, 2014Da farko dai wasu motoci ne biyu shake da bama-bamai suka tarwatse a Kazimiya da ke arewa maso yammacin birnin Bagadaza inda mutane 10 suka rasu tare da jikkata wasu 29, sannan wani ɗan ƙunar bakin wake ya tarwatsa motar sa a unguwar Talibiya cikin birnin na Bagadaza inda nan ma mutane tara suka rasu wasu kuma 26 suka jikkata, sai kuma a Mahmoudiyah da ke a nisan km 30 a kudancin binin na Bagadaza inda mutane aƙalla bakoye suka rasu.
A cewar Majalisar Ɗinkin Duniya aƙalla mutane 1100 ne suka mutu sakamakon hare-haren ta'addanci a ƙasar ta Iraƙi a watan Satumba da ya gabata, inda daga farkon watan nan na Oktoba kawo yanzu aƙalla wasu mutane 400 sun rasu sakamakon hare-haren.
Mawallafi: Salissou Boukari
Edita : Abdourahmane Hassane