Mutane da dama sun rasu a hare-haren Iraki
October 13, 2014Talla
Jami'an 'yan sandan suka ce biyu daga cikin hare-haren na kunar bakin wake ne kuma an kai su ne a birin Sadr yayin da aka kai cikon na ukun birnin Kadhimiyah lokacin da ake gudanar da shagulgulan bikin sallah da suka yi wa lakabi da Eid al-Ghadir.
Ma'aikatar cikin gidan Irakin da ta tabbatar da wannan labarin ta ce baya ga wanda suka rasu, da dama sun samu raunuka wasunsu ma munana kuma hare-haren sun wakana ne lokacin da jama'a ke tsaka da gudanar da harkokinsu.
Ya zuwa yanzu dai ba a kai ga tantance ko wacce kungiya ce ta kai wannan hare-hare ba ko ma dalilin yin hakan.