1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Harin kunar bakin wake yayin bukukuwan Sallah a Iraki

Lateefa Mustapha Ja'afarJuly 18, 2015

Masu aikin ceto na ci gaba da lalubo wadanda ke da sauran numfashi da kuma gawarwakin wadanda suka rasa rayukansu yayin harin kunar bakin wake da aka kai da mota a Iraki.

https://p.dw.com/p/1G0v4
Harin kunar bakin wake a Irak
Harin kunar bakin wake a IrakHoto: APTN

Harin kunar bakin waken da 'yan kungiyar ta'addan IS suka kai a wata kasuwa da ke birnin Khan Bani Saad na Irakin dai ya hallaka sama da mutane 110 mafiya yawansu Musulmi mabiya mazhabar Shi'a. Harin dai na zuwa ne a yayin da al'ummar Musulmin duniya ke kammala azumin watan Ramadana da kuma gudanar da bukukuwan karamar Sallah. Kungiyar IS ta bayyana cewa ita ke da alhakin kai harin a shafinta na Twitter. A baya-bayan nan dai dakarun sojojin Irakin da hadin gwiwar mayakan sa kai daga bangaren Musulmi mabiya mazhabar Shi'a da kuma na Sunna sun jajirce wajen ganin sun samu nasarar fatattakar 'yan ta'addan na IS daga gundumar Diyala.