Mutanen Laberiya na zaben shugaban kasa
October 10, 2017Talla
'Yan takara 20 ne dai ke zawarcin kujerar shugabancin kasar a halin yanzu, yayin da akalla 'yan takara dubu 1,000 ke naman shiga majalisar dokokin kasar. Kawo yanzu dai babu alamun manazarta da ke hasashen dan takaran da ka iya kaje shugaba Serlief har sai anje zagayen farko na zaben.
Kasar Laberiya dai ta sha fama da manyan matsaloli bayan mummunan yakin basasa na tsawon shekaru 14 da ya ta'azzara kasar, wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane sama da dubu 250, yayin da wasu milyan daya suka tsere daga kasar.
A yanzu dai masu sanya ido kan zaben daga kasashen ketere, na fatan Labaeriya su gudanar da zaben na yau a cikin lumana, da zai tabbatar da musayansar mulki cikin ruwan sanyi tsakanin fararen hula a kasar cikin shekaru 70 da suka gabata.