SiyasaArewacin Amurka
Mutum bakwai sun halaka a hadarin jirgin sama a Mexico
December 23, 2024Talla
Rahotanni dake daga yankin Jalisco dake yammacin kasar Mexico sun bayyana cewa akalla mutum bakwai sun halaka bayan faduwar wani karamin jirgi a cikin duhun daji. Jirgin mai lamba 207 ya baro garin La Parota ne na jihar Michoacan makwabciyar garin na Jalisco.
Tsamin dangantaka tsakanin Mexico da Amurka
Hukumomin garin sun fada a shafukan sada zumunta cewa hadarin ya auku ne a wani wuri mai wahalar isa. Tun da farko hukumar kare fararen hula ta garin ta bayyana cewa an kirga gawarwaki bakwai amma ba a iya tantance ko su wanene ba.
Zaman makokin mutuwar Shugaba Ebrahim Raisi na Iran
Hukumomi sun kara da cewa suna jiran zuwan masu binciken kwa-kwaf domin daukar gawarwakin kuma suka ce babu wani mutum da ya saura da ba a gani ba.