Mr Vitaly Churkin ya mutu a kasar Amirka
February 20, 2017Talla
Ma'aikatar harkokin kasashen ketare ta Rasha,ta sanar da mutuwar jakadan Rasha a Majalisar Dinkin Duniya Vitaly Churkin. Rahotanni sun nunar da cewa Churkin wanda ya kasance jakadan na Moscow mafi dadewa a Majalisar ta Dinkin Duniya ya mutu ne a yau a birnin New York na Amirka. Kawo yanzu dai babu cikakken rahoto dangane da sanadiyyar mutuwar tasa, sai dai alamu na nuni da cewa mutuwar tasa ta ta kasance ta bazata.