1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Myanmar ta kira MDD ta taimaka a dawo da 'yan Rohingya gida

Mohammad Nasiru Awal AS
March 14, 2018

Jami'an kasar Myanmar sun ce lokaci ya yi da hukumomin Majalisar Dinkin Duniya za su shiga cikin aikin mayar da dubun dubatan 'yan gudun hijirar Rohingya gida.

https://p.dw.com/p/2uKyc
Bangladesch | Rohingya-Flüchtlingslager rund um Cox's Bazar
Hoto: DW/ P. Vishwanathan

Daruruwa dubbai na 'yan Rohingya suka tsere zuwa kasar Bangladesh sakamakon cin zarafinsu a Myanmar.

Babban sakatare a ma'aikatar harkokin wajen Myanmar Myint Thu ya fada a wannan Laraba cewa ofisoshin hukumar kula da 'yan gudun hijira ta MDD da hukumar raya kasa ta MDD sun ba su amsa dangane da gayyatar da gwamnatin Myanmar ta yi musu, tare da ba da shawara yadda za a tafiyar da aikin. Ya ce yanzu haka mahukunta a Myanmar na nazarin wannan shawara.

Wani kakakin MDD a Myanmar ya tabbatar da batun kan yadda hukumomin MDD za su taimaka a samar da kyakkyawan yanayi na komawar 'yan gudun hijirar gida cikin lumana.

Sai dai masana sun ce ba za a iya tabbatar da tsaron lafiyar Musulmin Rohingya su kimanin dubu 700 da suka tsere zuwa Bangladesh bayan matakan ba sani ba sabo da dakarun tsaro suka dauka kansu a watan Agustan bara ba.