Nadin mataimakin shugaban Sudan ta Kudu
August 23, 2013Talla
Shugaban kasar Sudan ta Kudu Salva Kiir ya nada James Wani Igga, tsohon jigon 'yan tawaye a matsayin sabon mataimakin shugaba kasa.
Kamfanin dillancin labaran Faransa na APF, ya ruwaito cewa gidan rediyon kasar ya tabbatar da nadin Igga wanda ke zama kakakin majalisar dokoki tun shekara ta 2005. Wannan mataki ana ganin zai zama gada ta hada kan kabilun sabuwar kasar, wadda ta balle daga Sudan a shekara ta 2011.
Sabon mataimakin shugaban kasar ta Sudan ta Kudu Wani Igga, ya maye gurbin Riek Machar, wanda Shugaba Salvar Kiir ya cire, lokacin da ya rusa daukacin majalisar gudanarwar kasar.
Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Mouhamadou Awal Balarabe