1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nadin wasu shugabanni a Afirka sun dauki hankali a Jamus

Mohammad Nasiru Awal MA
October 26, 2018

Zaben shugabanni a wasu kasashen nahiyar Afirka, suna daga cikin manyan batutuwan da suka ja hankalin duniya a makon karshe na watan Oktoban nan.

https://p.dw.com/p/37FjD
Kamerun Präsident Paul Biya
Shugaba Paul Biya na kasar KamaruHoto: picture-alliance/Photoshot/Ju Peng

Za mu fara da jaridar Neue Zürcher Zeitung wadda a labarin da ta buga mai taken matan kasar Habasha sun yunkuro, ta fara da cewa Firaminista Abiy Ahmed na kara mai da hankali kan shugabancin mata. Ta ce a ranar Alhamis majalisar dokokin kasar Habasha a karon farko ta ga baki dayanta ta zabi mace a mukamin shugabar kasa. A hukumance yanzu Sahle-Work Zewde ita ce shugabar kasar da ke a yankin kahon Afirka ko da yake mukamin na kusan jeka na yi ka ne, domin ofishin Firaminista ke tafiyar da harkoki na shugabancin kasar.

Äthiopien Addis Abeba neue Präsidentin Sahle-Work Zewde
Sahle-Work Zewde, shugabar kasar HabashaHoto: Getty Images/AFP/E. Soteras

Sahle-Work dai ta kasance wakiliya ta musamman ta babban sakataren Majlisar Dinkin Duniya a kungiyar Tarayyar Afirka. Ta taba rike mukamin jakadar Habasha a Faransa da Jubuti da kuma Senegal. Jaridar ta ce zaben Sahle-Work a mukamin shugabar kasar ya dace da manufofin sauyi na Firaminista Abiy, wanda yanzu haka ya ba wa mata da dama mukamai a majalisar ministocin kasa ciki har da na sabuwar ministar tsaron kasa wato Aisha Mohammed.

Jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung ma ta yi tsokaci kan zabe, musamman sake zaben Paul Biya a matsayin shugaban kasar Kamaru. Ta ce Paul Biya zai ci gaba da zama a fadar shugaban kasa yayin da rikici a kasar ke rincibewa. Ba wanda ya yi mamaki na sakamakon zaben da aka bayyana a ranar Litinin da ya ayyana shugaba Paul Biya mai shekaru 85 a matsayin wanda ya lashe zaben ranar 7 ga watan Oktoba da kimanin kashi 71 cikin 100 na yawan kuri'un da aka kada.

Kamerun Präsidentschaftswahlen Präsident Paul Biya
Shugaba Paul BiyaHoto: Getty Images/AFP/A. Huguet

Abokin takararsa Maurice Kamto wanda bayan zaben ya yi shailar samun nasara, ya tashi da kaso 14 cikin 100. Jaridar ta kara da cewa Shugaba Biya wanda nan da makonni biyu zai sha rantsuwa yin sabon wa'adin mulki na shekaru bakwai, zai ci gaba da fuskantar rikice-rikice na yankin Ambazoniya, wanda ke neman ballewa daga Kamaru saboda dalilai na mayar da su saniyar ware, rikice-rikicen kuma da babu alamun cewa Shugaba Biya zai iya magance su.

Ita kuwa jaridar Neues Deutchland ta leka kasar Angola tana mai cewa shugaban kasa Joao Lourenco wanda a bara ya kama ragamar mulkin kasar ya dukufa wajen yaki da matsalr cin hancin da rashawa a daidai lokacin da kasar ke cikin wata tattaunawa mai wahala da Asusun Lamuni na Duniya wato IMF.

Berlin Joao Lourenco Präsident Angola
Shugaba Joao Lourenco na kasar AngolaHoto: DW/Cristiane Vieira Teixeira

Jaridar ta ruwaito kungiyoyi masu zaman kansu na yabon yadda sabon shugaban ke nuna halin ba sani ba sabo a kokarin kawar da matsalar ta cin hanci da rashawa. Angola mai arzikin man fetir tana fama da matsalar karancin kudi saboda haka Shugaba Lourenci ke tattaunawa da Asusun IMF, amma dole ya yi taka tsakantsan musamman dangane da kudin ruwa mai yawa daga bashin da Angolar za ta ciyo daga IMF.