1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar: Amurka na son a fifita diflomasiyya

August 11, 2023

Yayin da kungiyar ECOWAS ta bukaci dakarunta da su zama cikin shirin ko-ta-kwana don dawo da hambarariyar gwamnatin Nijar, Amurka ta sake jaddada matsayarta ta a fifita hanyoyin diflomasiyya domin tunkarar lamarin.

https://p.dw.com/p/4V1ji
Hoto: Darren England/AAP/dpa

Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken ne ya bayyana hakan a daren Alhamis jim kadan bayan kammala taron shugannin kasahsen kungiyar raya tattalin arzikin kasashen Yammacin Afrika karo na biyu da aka gudanar a birnin Abuja na Najeriya.

A cikin sanarwar da babban jami'in diflomasiyyan ya fidda, ya yaba da duk irin matakan da kungiyar EOWAS ko CEDEAO ta ce za ta ba wa fifiku don dawo da dimokuradiyya a Nijar cikin ruwan sanyi.

Kasashen na ECOWAS dai sun sha alwashin ci gaba da yi wa Nijar matsin lamba ta hanyar takunkumai matsin tattalin arziki, yayin da majalisar sojojin da ta yi juyin mulki ke nuna alamu na tsayuwar kwamen jaki kan karbar tayin kungiyar na dawo da hambararren shugaba Mohamed Bazoum kan kujerarsa.