Rudu a 'yancin majalisun jihohin Najeriya
June 9, 2020Duk da cewar sashi na 121 na kundin tsarin mulkin Tarayyar Najeriya ya tanadi 'yancin cin gashin kai ga majalisun dokoki da bangaren shari'a na jihohin kasar, karfin fada ajin gwamnonin ya hana aiwatar da wannan sashe mai tasiri ga makomar dimukuradiyyar kasar.
Wani yunkuri a bangaren fadar gwamnatin kasar da ta fitar da umarni na yin hakan dai, ya janyo murna cikin Najeriyar da ke fatan 'yancin na iya kai wa ga samar da ingantaccen tsarin dimukuradiyya a daukacin matakai na gwamnatin kasar guda uku.
To sai dai kuma matsin lamba daga gwamnonin kasar na shirin mayar da hannun agogo baya, a Najeriyar da ta dauki lokaci tana neman 'yanci na ragowa na bangarorin mulkin guda biyu na jihohin, amma kuma ba nasarar har ya zuwa yanzu.
An jima ana dako
Tun daga Obasanjo zuwa ga gwamnatin marigayi Umaru 'Yar Adua da ma ta tsohon Shugaba Goodluck Jonathan dai, an dauki lokaci ana fafutukar tabbatar da 'yancin 'yan dokar ba tare da kai wa ya zuwa nasara ba. Kafin sabon umarni na 10 da a karkashinsa shugaban da ke kai yanzu ya ce ko dai gwamnonin su mika wuya ga tabbatar da 'yancin kisan kudin, ko kuma kwamitin rabon kudin kasar ya hana musu nasu.
Wani taro a tsakanin wakilan gwamnonin da shugaban kasar ya kama hanyar mayar da tsarin gidan jiya, tare da bai wa gwamnonin nasarar dakatar da shirin da masu sharhi ke fatan ka iya kai wa ga bude danba ta tabbatar da dimukuradiyya mai tasiri cikin kasar.
Akwai sauran aiki
Kayode Fayemi dai na zaman shugaban kungiyar gwamnonin kasar, da kuma ya ce da akwai sauran gyara a cikin sabon tsarin na gwamnatin ta Abuja.
Ana dai zargin komawar da dama a cikin majalisun dokokin da ma alkalai na jihohin ya zuwa 'yan amshin shata maimakon sauya makomar al'umma a jihohinsu, a cikin tsarin da ke bukatar sauyi a ko'ina. Kuma a tunanin Barrister Buhari Yusuf da ke zaman wani lauya mai sharhi, a batun dokokin kasar ana bukatar jan aiki a bangaren Shugaban Buhari kafin mika wuyan gwamnonin da ke kisa suna shan romo a cikin tsarin na yanzu.