Najeriya: Boko Haram ta sace yara 1000
April 13, 2018Talla
Cikin wannan alkaluman da Asusun ya fitar, har da 'yan matan sakandaren garin Chibok 276 da aka sace a shekara ta 2014. An tattaro alkaluman ne bisa bayanan da aka samu ko kuma wadanda aka sanar da labarin batansu. Wannan na zuwa ne a yayin da ake shirin taron tunawa da sace 'yan matan garin na Chibok shekaru hudu da suka gabata a jahar Borno, da ke yankin Arewa maso Gabashin Najeriya.
Akwai malaman makaranta dubu biyu da 295 da suka rasa rayukansu acewar Asusun, kuma har yanzu ba a daina kai hare-hare ko sace-sacen yara a yankin ba, lamarin da Asusun na UNICEF ya baiyana hakan da wani abin takaici ga irin barazanar da rayuwar yara kanana ke fuskanta a Najeriya.