Sa ido kan amfani da kafofin sada zumunta a Najeriya
October 30, 2019Bayan daukar tsawon lokaci tana yunkuri na kafa dokar da za ta sanya ido a kan amfani da kafofin sada zumunta a kasar, a yanzu gwamnatin tarayyar Najeriya ta sake fitowa fili tare da bayyana cewa ya zame ma ta tillas ta taka wa masu amfani da kafofin sada zumunta birki, saboda abin da ta kira wuce iyaka na yada labaru na karya da gwamnati ta ce sanya ido a kyale su zai iya jefa kasar cikin mumunan hali. Mr. Lai Mohammed shi ne ministan yada labaru da al'adun gargajiya na Najeriya da ya bayyana yadda gwamnatin ke son yi.
"Ba gwamnatin da ta san abin da take yi za ta kyale ta bari labarun karya su haifar mata da matsala da haddasa rikici. Shi ya sa ya zama dole mu dau mataki mu shawo kan wannan lamari."
To sai dai tuni wannan ya sanya mayar da martani da ma bayyana ra'ayoyi mabambanta a kan halarci, amfani da ma akasin yin hakan bisa sanin abinda ke faruwa a Najeriya a ka wannan batu na amfani da kafafan sada zumunta. Shuaibu Leman shi ne sakataren yada labaru na kungiyar ‘yan jaridu ta Najeriya da ya ce "matukar gamnati ta daki wannan mataki to ko ba dade ko ba jima abin zai ga 'yan jarida." Ya kara da cewa a yanzu 'yan jarida a Najeiya na cikin hali na tsoro saboda "a kullum mahukunta na kokarin bullo da hanyoyin muzuguna wa 'yan jarida."
Ko da yake har yanzu babu cikakken bayani a kan yadda dokar za ta kasance, amma a baya gwamnatin na duba sanya tara ta miliyan biyar ga kafofin yada labaru da suka yada labaru na karya. Shi kuwa Salihu Dantata Mahmoud daya daga cikin 'ya'yan kungiyar kare hakin jama'a da wanzar da zaman lafiya na mai bayyana cewa.
"A matsayinmu na masu kare hakin dan Adam ba mu yi na'am da wannan mataki da gwamnatin Najeriya za ta dauka kan taka wa masu amfani da kafafan sada zumunta biriki ba."
Batun yada labaru na karya da nuna kyama ga wani sashi, kabila ko alu'mma da kafofin sada zumunta ke yi babbar matsala ce, don ta kai ga gwamnatin kaddamar da shiri na musamman domin shawo kan matsalar. To sai dai ga Adamu Attahiru na kungiyar masu amfani da kafofin sada zumunta ya bayyana yadda suke kalon lamarin.
"Babu shakka dokar da gwamnatin ke son kawowa don tsabtace harkar kafofin sada zumunta abu ne mai kyau. Domin hakan zai taimaka wajen zakulo masu amfani da wadannan kafafan a hanyoyin da ba su dace ba."
A baya dai gwamnatin Najeriya ta yi kokarin kafa doka a kan amfani da kafofin sada zumunta da ma yunkuri a majalisa da al'ummar kasar suka bijire masa. Yanzu dai abin jira a gani shi ne ko a wannan karon gwamnatin za ta samu nasarar kafa dokar kula da kafofin sada zumunta a kasar.