1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Fargabar tsaro a Najeriya yayin bukukuwa

December 23, 2020

Hukumar Tsaro ta Farin Kaya a Najeriya wato DSS, ta fitar da wata sanarwa na yiwuwar kai wa Coci-coci hare-haren bama-bamai lokacin shagulgulan bikin Kirsimeti da na sabuwar shekara.

https://p.dw.com/p/3nAUH
Symbolbild | Nigeria | SWAT
Fargabar tsaro yayin bukukuwan Kirsimeti da sabuwar shekaraHoto: Imago Images/ZUMA Press/Planetpix/A. F. E. Lii

A wata takarda da aka rarrabawa manema labarai da Hukumar Tsaron Farin Kaya ta Kasa DSS ta fitar, ta bayyana cewa ta gano wani shiri da wasu bata gari ke yunkurin aiwatarwa, na sanya bama-bamai a wuraren da ake taron jama'a a fadin kasar yayin shagulgulan bikin Kirsimeti da na sabuwar shekera. Kakakin hukumar na kasa Peter Ifunanya ya sanar da hakan, inda kuma ya yi kira ga daukacin ‘yan Najeriya da su farga kuma su fadawa jami'an tsaro duk wani abu da suka gani ba su gamsu da shi ba.

Karin Bayani:Najeriya na fafutukar yaki da ta'addanci

Tuni dai kungiyar Kirstoci ta Kasa a Najeriyar wato CAN, reshen jihar Kaduna ta mayar da martini kan wannan batu, inda kuma ta bukaci ganin an samar da isassun jami'an tsaro ta ko'ina a fadin kasar domin kare rayuka da duniya. Shugaban kungiyar Kiristocin jihar Kaduna Rev. John Joseph Hayab ke cewa suna bukatar ganin dukkanin masu ruwa da tsaki a bangaren tsaro sun ribanya kokarin da suke yi domin magance duk wata barazanar farmaki. 

Nigeria Angriffe von Extremisten
'Yan bindiga na yawan kai farmaki a yankin Arewa maso Yammacin NajeriyaHoto: picture-alliance/dpa

Shugaban Kiristocin ya kuma shawarci 'yan uwansa da su rage cinkoso su kuma bi matakan kaucewa kamuwa da cutar coronavirius. Ya ce sun umurci dukkanin malaman Coci-coci da su tabbatar da ganin sun rage yawan lokacin da ake amfani da shi wajan sujada su kuma ja hankalin mabiya a kan sanya takunkumin rufe fuska da wanke hannu akai-akai tare da bayar da tazara tsakakin alumma.

Karin Bayani: Muhawara ta barke a kan batun tsaro a Najeriya

Imam Dr. Muhammad Nurayn Ashafa shi ne shugaban kungiyar Kyautata Fahimyatar Juna Tsakanin Mabanbamta Addinai a Najeriya, ya kuma bayar da shawarwari kan matakan magance wadannan hare-haren. Ya kara da janyo hankalin alumma a kan bin dokokin da hukumomin tsaro suka shimfida domin kaucewa asarar rayuka da dukiyoyi, kana mabiya su kai rahotan duk wani abun da ba su gane masa ba. Ya zuwa wannan lokaci dai, tuni matasa Musulmi suka fara aikawa abokanansu Kiristocin sakonnin barka da bikin Kirsimeti da na sabwar shekarar domin kara kulla kyakkyawar dangantaka da nufin kawo kashen rigingimun kabilanci da siyasa da na addinai.