1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus da Najeriya na yaki da hijirar matasa

Uwais Abubakar Idris AH
February 6, 2024

Ministar kula da ayyukan raya kasa ta kasar Jamus Svenja Schulze ta kaddamar da cibiyar kula da hijira ta hanyar da ta dace a kokari na shawo kan matsalar hijira da matasa ke yi ta haramtacciyar hanya.

https://p.dw.com/p/4c625
Svenja Schulze ministar kula da ci gaba ta kasar Jamus
Svenja Schulze ministar raya kasa ta JamusHoto: Uwaisu Idris/DW

 Wannan dai wani sabon tsari ne ko kuwa dubara da gwamnatin kasar Jamus ta bullo da shi, inda gwamnatin kasar Jamus ta samar da cibiya inda ake tantance fanonin na kwarewa da matasa ke da shi domin sama masu guraben ayyuka a kasar Jamus ko kuma in a Najeriyar suke son aiki, sannan a daya bangaren wadanda ke zaune a Jamus ke son dawowa Najeriya suma sai a sama musu guraben ayyukan yi. Nkeiruka Onyejeocha ita ce minister kasa a ma'aikatan kwadago da ayyukan yi ta Najeriya ta bayyana tasirin samar da cibiyar  tun 2018 ta fara aiki.

Dalilan Jamus na samar da cibiyar

Svenja Schulze da Nkeiruke Onyekeocha minista kwado da raya kasa ta Najeriya
Svenja Schulze da Nkeiruke Onyekeocha minista kwado da raya kasa ta NajeriyaHoto: Uwaisu Idris/DW

Ministar kula da dangantar tattalin arziki da ci gaban kasar Jamus wacce ta kadammar da wannan cibiya a unguwar Karu da ke jijhar Nasarawa ta bayyana dalilan da suka sanya Jamus samar da cibiyar wacce tuni suka yi irinta a kasar Morocco. Ta ce: ''Kaura abu ne na zahiri da ya kamata a tsara shi yadda zai amfani kowa, daga wadanbda suke hijirar da kasarsu da ma kasar da za su je. A wannan cibiya wuri ne da masu son hijira suke zuwa da fatan da suke da ita, da kwarewarsu inda sukje samun bayanai a kan damar da ke akwai a Najeriya da Jamus''.

Samar da aiki wa matasa a Jamus da Najeriya

Svenja Schulze ministar raya kasa ta Jamus
Svenja Schulze ministar raya kasa ta JamusHoto: DW

Tun da farko mataimakin gwamnan Jihar Nasarawa Dr Emmanuel Akabe ya bayyana muhimmancin samar da cibiyar yana mai yaba wa danganataka tsakanin Najeriya da kasar Jamus. Mata dai na cikin wadanda aka fi cin zarafinsu a dalili na kaura ta haramtacciyar hanya. Hon Margaret Elayo  ita ce kwashiniyar kula da harkokin jin kai da ayyuta na musamman a Jihar Nasarawa. Kasashen Jamus da Najeriya na fatan samar da cibiyar ya bude karfafa samun ayyukan yi ga masu sha'awar kaura tun daga nan Najeriya da wadanda ke son  dawowa gida Najeriya.